4 Agusta 2020 - 12:10
Zan Bada Fifiko Ga Gyara Tsarin Warware Rikicin WTO, Inji ‘Yar Takarar Najeriya

'Yar Nijeriya mai neman takarar shugabancin hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) wato Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce idan aka zabe ta, za ta mayar da hankali kan gyara tsarin warware rikici na hukumar.

ABNA: Cikin wata tattaunawa da ta yi a baya-bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Ngozi Okonjo-Iweala dake takarar tare da wasu mutum 7, ta ce abubuwan da za ta ba fifiko idan aka zabe ta sun hada da; shiryawa taron ministocin kasashen hukumar karo na 12 da za a yi badi a Kazakhstan, da farfado da tsarin warware rikici da kuma gyara kundin ka'idojin hukumar.

Yanzu haka, tsarin warware rikici na hukumar ya yi rauni. Kamata ya yi a ce, kungiyar wadda ke zaman kotun kolin warware rikice-rikicen cinikayya, na da akalla alkalai 7, inda ake bukatar alkalai 3 a mataki mafi karanci domin ta yi aiki.

Sai dai, gwamnatin Amurka ta shafe sama da shekaru 2 tana hana sabbin nade-nade, inda jami'an kasar ke ikirarin kotun na wuce huruminta.

Tsohuwar ministar kudin ta Najeriya, Ngozi Iweala ta ce za ta mayar da hankali ne wajen gyara tsarin warware rikici, saboda shi ne kashin bayan hukumar.

Ta ce idan ka'idoji ne ke tafiyar da hukuma, dole ne a samu inda za a sulhunta, tana mai cewa, a don haka, farfado da tsarin warware rikici zai zama abun da za ta mayar da hankali kai.

342/